For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Alhaji Ahmadu Haruna Zago Shi Ne Shugaban Jam’iyyar APC Zababbe ­– Shekarau

A cigaba da sa’insar da ake kan shugabancin jam’iyyar APC a jihar Kano, tsohon Gwamnan jihar kuma Sanata mai ci, Sanata Ibrahim Shekarau ya magantu kan matsayarsa da wadanda ke tare da shi.

Tsohon Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wani rubutu da ya fitar a shafinsa na Facebook mai suna Ibrahim Shekarau.

Ya yi jawabin ne tare da mika sakon barka da zagayowar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SallalLahu Alaihi wa Sallam ga al’ummar Musulmin Najeriya.

“Da farko ina amfani da wannan lokaci na taya duk al’ummar Musulmi farin cikin zagayowar ranar da aka haifi Manzon Allah SAW, wacce gwamnatin tarayyar Najeriya a jiya ta ware a matsayin rana ta musamman don tunawa da ita.

“Annabi Muhammadu SAW shi ne mafi kaunarmu a duniya, bawan Allah da muke shaukin samun cetonsa a lahira. Hallita ta kebantacciya a gurin Allah da muke kokarin koyi da ita. Allah ya kara wa Manzon Allah SAW daraja da wasila fil Jannati.

Tsohon gwamnan ya kuma waiwaici maganar rikicin shugabancin jam’iyyarsu ta APC a jihar Kano inda ya ce, “ni Sanata Ibrahim Shekarau, na jagoranci  wasu daga cikin wadanda aka zabe mu, daga majalisar kasa. Mun shigar da kuka ga uwar jam’iyya akan rashin gudanar da abubuwan da suka shafi jam’iyya tare damu. Mu zababbu ne, jama’armu suna da hakki. An karbi korafinmu da mutumtawa, kuma mun gode. Muna fatan a warware takaddamar cikin lumana.

“Ina sanar da duk jama’armu, ina cikin jam’iyyar APC daram-dam, zamu tsaya har illa Masha Allahu. A wannan tafiya tamu babu cin mutunci, babu zagi, ba wulakanci. Mun yi hakuri amma ba zamu lamunci sakarci ba. Korafinmu yana gaban mahukunta. Ba zamu saurari kowa ba sai wadanda muka kai musu kuka.

“A jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago shi ne shugaban jam’iyyar APC zababbe a gurinmu. Muna yi masa addu’ar Allah ya karfafi zuciyarsa kuma Allah ya  taya shi riko. Sauran wadanda aka zabesu tare da shi su 35 muna addu’ar Allah ya yi musu jagora.”

Idan za a tuna, a ranar Asabar da ta gabata ne aka gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar APC na jihohi wanda ya bar baya da kura a jihohi da dama.

A jihar Kano dai bangaren gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje, sun taru kuma sun zabi shugaban jam’iyyar mai ci a matsayin wanda zai ci gaba da jagorancin jam’iyyar a jihar.

Yayin da bangaren tsohon gwamna Shekarau da ke da goyon bayan wasu ‘yan majalissun tarayya suka taru suka zabi Ahmadu Haruna Zago a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano.

Akwai dai rahotannin da ke nuni da cewa uwar jam’iyyar APC ta kasa za ta iya mutunta wadanda gwamnonin jihohi suka goyi baya tare da watsi da wadanda ke adawa da gwamnonin.

Comments
Loading...