Yayin da jama’a ke ci gaba da hasashen yadda babban zaben kasar na 2023 zai kasance, an gano wata fostar yakin neman zabe ta shahararren mawakin nan na masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Ali Isa Jita.
Fostar wadda abokiyar sana’arsa Rahama Sadau ta wallafa a shafinta na Instagram, ta nuna cewa mawakin zai fito takarar kujerar gwamnan jihar Kano ne a zaben na 2023.
KU KARANTA: Dan Wasan Hausa Sani Garba SK Ya Rasu A Kano
Sai dai kuma babu suna ko tambarin wata jam’iyyar siyasa a cikin hoton wanda ke dauke da rubutu kamar haka: ‘hangen nesa, sha’awa, aiki Jita 2023, Ali Isa Jita don neman gwamna, jihar Kano, Insha Allah’.
Jarumar ta kuma wallafa fostar dauke da rubutu da tayi tana cewa “Ehem Ehem” da “Abu A Gidanmu”.
Daga: Legit Hausa