For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Amaechi Zai Iya Zama Zabin Buhari A 2023

Ministan Sufuri wanda tsohon Gwamnan Jihar Rivers ne na jiran lokacin da ya dace domin bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC.

Wakilin PUNCH ya gano cewa, wadansu ‘yan Arewa na kusa da Shugaban Kasa sun yarda cewa, Amaechi ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar APC da kuma kasancewar Buhari Shugaban Kasa a 2015.

Wani wanda ke da alaka da maganar ya bayyana cewa, “Ka san ba don gudunmawar da Amaechi ya bayar ba a matsayinsa na Shugaban Kungiyar Gwamnoni a wancan lokacin wadanda suka kafa sabuwar PDP, inda 5 daga cikinsu suka dawo jam’iyyar APC, da yanzu babu APC.”

Majiyar ta kara da cewa, “Shugaban Kasa ya amince da shi a matsayin Daraktan Yakin Neman Zabensa har sau biyu, wannan abun dubawa ne sosai. Kar kuma ka manta cewa, shi ke rike da ma’aikatar da aiyukanta suka fi muhimmanci a lokacin Buhari. Duk wannan na nuni da karfin guiwar da Shugaban Kasa yake da shi a kansa.”

Majiyoyi sun nuna cewa, Amaechi yana taka-tsan-tsan wajen kula da yanayin Shugaban Kasa da sauran masu neman mulki kafin ya bayyana kudirinsa na takarar Shugaban Kasa.

KU KARANTA: Sarkin Daura Zai Nada Ameachi Dan Amanar Daura

Akwai kuma rade-radin cewa, Amaechi wanda za a yiwa sarautar Dan Amanar Daura a Fadar Sarkin Daura, ranar 5 ga Fabarairu, 2022 zai yi amfani da irin tarbar da zai samu domin gane irin karbuwarsa a yankin Arewa.

Sarautar da za ai masa wadda take nufin ‘wanda aka amincewa’ na nuni da irin kusancinsa da Shugaban Kasa da kuma nuna jindadi game da biyayyarsa ga Shugaba Buhari tun shekarar 1998.

“Taron da za ai a Fadar Sarki zai zama hanyar gwada farinjininsa da kuma karbuwarsa a kan kudirin takarar Shugaban Kasar da bai bayyana ba. Sarautar kanta na nuni da gamsuwar Masarautar Daura da shi, musamman saboda aiyukan da ma’aikatarsa ta yi jihar Katsina,” in ji majiyar.

(PUNCH)

Comments
Loading...