Daga: Ahmed Ilallah
Koda yake, dama kamar yadda tarihi ya nuna an kafa Hadejia ne, a cikin Tafkin Chadi, wurare irin su Hadejia na cikin yankin tafkin Chadi da ya kafe.
Inda za a ce Tafkin Chadi zai koma yadda ya ke a baya da tabbas ba za a samu garuruwa irin su Hadejia, Birniwa, Kiri Kasmma da dubban kauyukan su ba.
Kusan a wannan shekarun da duniya baki daya take fama da matsalar dumamar yanayi da chanjin yanayi, yankin Hadejia ba a barshi a baya ba wajen fuskantar wannan matsalar.
Kusan a yanzu duk lokacin da a ka samu masifar ambaliyar ruwa, ana asarar rayuka masu yawa, ga asarar gonaki da gidaje da kuma dukiya mai tarun yawa.
Abin mamaki kullun barazanar ambaliyar ruwannan karuwa take yi, hawhawa take yi, ta bana tafi ta bara.
A shekara ta 2020 a tskanin watan Augusta zuwa October, ambaliyar ruwa ba karamar barna ta yi ba, kama daga asarar rayuka da dukiyoyi, wannan ambaliya har tayi barazanar tada Birnin Hadejia.
Majalissar Dinkin Duniya a binciken ta karkashin Group on Earth Observation (GEO), “sakamakom duba na tauraron Dan Adam a kan chanjin yanayi, alkaluma sun nuna cewa, a nan da shekaru biyu masu zuwa a kwai yiyuwar samun gaftarewar kasa a garuruwan Auyo, Birniwa da Hadejia”.
Kamar yadda daya daga cikin wakilan Majalissar Dinkin Duniyar a fannin Chanjin Yanayi Mr. Nura Jibo ya fada kamar a shekara ta 2020 “…matsalar Hadejia da ban take, ita Hadejia ta fado ne a kasan Hadejia Jama’are River Basin da kuma Kwamadugu Wetland, da ma garin (Hadejia) ya na kan hanyoyin da ruwa ya ke kangarawa zuwa Lake Chard” ya kara da cewa “babu wata dabara da ta ragewa mutanen wannan yaki, face tunanin chanja matsagunni”
Duk da ksancewar akwai shawarwari da aka bada, musamman mutanen wannan yankin a kan su yawaita dasa bishiyoyi, amma kokarin a wannan fannin yayi karanchi.
A wannan shekarar ma fa, barazanar wannan ambaliyar tafi ta wadda ta gabata, domin tun kafin a ce ruwan ya gama zuwa, kauyuka da dama sun tashi, a wasu wuraren an samu asarar rayuka, gonaki da dama ruwa ya shanye su, dubban mutane sun bar gidajen su, a wannan karon hatta makarantun gwamanti ma ruwa ya ci su.
Lokaci yayi fa, da masu fada a ji da hukumomin gwamnati ya kamata su sake bibiyar wannan ruhoton don yin abin da ya kamata.
Mutanen Hadejia ya kamata ku soma yin tunanin yin taswirar sabon birnin Hadejia a arewacin Hadejia, dama an ce turawan Ingila da suka zo sun bada wannan shawara.
alhajilallah@gmail.com