For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3 Ta Kuma Rusa Gidaje 495 A Kano

Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu sannan gidaje 495 suka rushe biyo bayan mamakon ruwan sama a Karamar Hukumar Ajingi ta Jihar Kano.

Shugaban Hukumar Kula da Bukatun Gaggawa na jihar, Saleh Jili ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Ya bayyana cewa, tawagarsa ta je Ajingi ne domin jajantawa wadanda abun ya rutsa da su a madadin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

Ya ce al’amarin ya faru ne bayan samun mamakon ruwan sama a ranar 3 ga watan Agustan da muke ciki, inda gidaje 495 suka rushe sannan kuma mutane uku suka rasu, ciki har yarinya ‘yar shekara 4.

Jili ya kuma bayyana guraren da abun ya faru da suka hada da Toranke, Kara Malama, Chuna da kuma Balare a Karamar Hukumar Ajingi.

Ya ce, a matsayin matakin gaggawa, tawagar zata mika kayan tallafi ga shugaban kwamitin samar da agajin gaggawa na Karamar Hukumar Ajingi domin ya gaggauta rabawa ga iyalan wadanda suka rasu da kuma wadanda suka sami raunuka.

Ya kara da cewa, zai mika cikakken rahoton lamarin ga gwamnati bayan kammala binciken da jami’an da aka tura zasu yi, domin daukar mataki nan take.

Ya bayar da shawara ga mazauna garuruwan da su dinga kwashe magudanan ruwa, da kuma shawartar mazauna kusa da kogi a jihar da su canza gurin zama tare da sanar da SEMA domin samun dauki.

Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Ajingi, Sa’ad Ibrahim Toranke, ya yabawa gwamnatin jihar da kuma hukumar a bias karamcin da suka nuna musu.

Kayan tallafin da aka raba sun hada da shinkafa, masara, siminti, kwanon rufi, kusoshi, man girki, matasankai, wake da katifu da kuma sauransu.

Comments
Loading...