Daga: PUNCH
Kasar Amurka ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashe masu tauye damar yin addini, yayin da ta sanya Rasha, China da wasu kasashe takwas a matsayin kasashe na musamman da aka sawa ido saboda aiyukan da ke gudana na tauye hakkin yin addini a cikinsu.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba mai taken “‘Yancin yin Addinin da Mutum ya ga Dama”.
A shekarar 2020, kasar Amurka ta sanya Najeriya da wasu kasashe shida cikin jerin kasashe na musamman da suka shiga ko kuma suka amince da cin zarafin zabin addini, sai dai kuma Najeriya ba ta cikin jerin kasashen da aka sanya a cikin shekarar bana (2021).
Blinken, wanda a halin yanzu yana kasar Kenya da ke Gabashin Afirka domin ziyarar aiki, an shirya kai ziyararsa Najeriya a cikin wannan mako inda zai gana da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, da sauran mambobin majalisarsa.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, a cikin sanarwar da ya bayar a ranar Laraba, ya ce, “Amurka ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da goyon baya kan ‘yancin yin addini ko imani ga kowa da kowa a kowace kasa. A wurare da yawa a duniya, muna ci gaba da ganin gwamnatoci suna tursasawa, kamawa, yi wa mutane barazana, daure su, da kuma kashe mutane kawai don sun yi rayuwarsu daidai da addinin da sukai Imani da shi. Wannan Gwamnatin ta himmatu wajen tallafawa yancin kowane mutum na ‘yancin yin addini ko imani, gami da fuskantar da yaki da masu take hakkin na dan adam.
“Kowace shekara Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka tana da alhakin tantance gwamnatoci da ‘yan kungiyoyin da ba gwamnati ba, wadanda, saboda tauye ‘yancinsu na addini, sun cancanci sanya su a karkashin Dokar ‘Yancin Addini ta Duniya.
“Ina sanya kasar Burma, China, Eritriya, Iran, DPRK, Pakistan, Rasha, Saudi Arabia, Tajikistan, da Turkmenistan a matsayin kasashen da suka shiga jerin kasashe da za a sawa ido kan abubuwan da suke gudana na tauye hakkin ‘yancin yin addini.”
“Ina kuma sanya gwamnatocin kasar Aljeriya, Comoros, Cuba, da Nicaragua a cikin jerin sa ido na musamman ga gwamnatocin da suka tsunduma ko kuma suka kyale gudanuwar “munanan take hakkin ‘yancin yin addini.” A karshe, ina ayyana al-Shabab, Boko Haram, Hayat Tahrir al-Sham, Houthis, ISIS, ISIS-Greater Sahara, ISIS-West Africa, Jamaat Nasr al-Islam wal-Muslimin, da kuma Taliban a matsayin kungiyoyin da suke take hakkin yin addini.
“Kalubalen ’yancin yin addini a duniya a yau ya kasance na tsararre na musamman. Akwai shi a kowace kasa. Matsalar tana bukatar ci gaba da sadaukarwar duniya daga duk wadanda ba sa goyon bayan nuna kiyayya, rashin hakuri, da tsanantawa a matsayin da ake ciki. Akwai bukatar kulawar gaggawa ta kasashen duniya.
“Za mu ci gaba da matsawa duk gwamnatocin da su gyara kurakurai a cikin dokokinsu da ayyukansu, da kuma tabbatar da alhaki ga wadanda ke da hannu wajen cin zarafi. Kasar Amurka ta ci gaba da jajircewa wajen yin aiki tare da gwamnatoci, kungiyoyin jama’a, da membobin al’ummomin addinai don ciyar da ‘yancin yin addini a duniya da kuma magance matsalolin mutane da al’ummomin da ke fuskantar cin zarafi, da wariya saboda abin da suka yi Imani da shi, ko abin da ba su yi Imani da shi ba, ko mene ne.”