Shugaban Amurka, Joe Biden ya bukaci wasu daga cikin shugabannin kasashen Afirka da suke shirin gudanar da zabe a shekara mai zuwa da su tabbatar da cewar an gudanar da zabe mai ingancin da duniya zata amince da shi.
Biden ya bayyana hakane lokacin da ya gana da wasu shugabannin kasashe guda 6 a Washington wadanda kasashensu zasu gudanar da zaben shugaban kasa a shekarar 2023 ciki har da Shugaba Buhari na Najeriya da takwarorinsa na kasashen Congo, Gabon, Liberia, Madagascar da kuma Saliyo.
Mai baiwa shugaba Biden shawara akan harkokin tsaro Jack Sullivan ya ce, ganawar ba wai tana nufin Amurka na da fargaba bane dangane da zaben wadannan kasashe, sai dai bukatar taimaka musu wajen ganin an ci gaba ta fannin dimokiradiya.
Kasar Amurka ta kuma jinjinawa shugaban kasar Congo Tshisekedi saboda amincewar da yayi a gudanar da zabe a kasarsa a shekara mai zuwa, abinda ya sa Amurkar ta ba shi taimakon Dala miliyan 13 domin shirin zaben.
RFI Hausa