A jiya Laraba ne Majalissar Zartarwa ta Kasa ta amince da bayar da damar kasancewa ‘yan Najeriya ga ‘yan kasashen waje mutum 385 da ke zaune a kasar.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya ce, mutane 317 cikin masu neman kasancewa ‘yan Najeriya an amince musu ne bisa dalilin dadewa a Najeriya, yayinda kuma aka amincewa mutane 68 zama ‘yan Najeriya ta hanyar rijista.
Ya kara da cewa, wadanda aka amincewan sun cika dukkan ka’idojin da aka shimfida domin kasancewa ‘yan Najeriya.
Ministan ya kuma ce, Majalissar ta kuma amince da tsarin gano gobara na musamman da za a sanya a dukkan ofisoshin kashe gobara da ke fadin kasar nan.
Ya ce, tsarin ba zai ci ko sisin kobon gwamnati ba, sannan kuma za a yi shi ne a kan tsarin ci gaban fasahar sadarwa domin samun damar magance tashin gobara cikin gaggawa.