For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Bayyana Yiwa INEC Katsalandan A Matsayin Illa Ga Demokaradiyya

Kwamishinan Zabe na Jihar Ogun, Olusegun Agbaje, ya ce hukumar ba ta bukatar goyon bayan Majalisar Dokoki ta kasa da kuma amincewar Hukumar Sadarwa ta Kasa don shirin tura sakamakon zabe ta hanyar na’ura.

Agbaje ya fadi hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake magana a taron manema labarai a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zabe a jihar.

Ya soki matsayin Majalisar Dokoki ta kasa na cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ba ta da hujja a tsarin mulki wajen tura sakamakon zabe ta hanyar na’ura ba tare da amincewar NCC ba.

Majalisar dai ta dage kan cewa dole ne hukumar ta nemi amincewar NCC kafin ta mika sakamakon zaben ta hanyar na’ura.

Agbaje, ya bukaci ‘yan majalisun tarayya da kada su hana INEC yin aikin ta na tsarin mulki.

A cewar Agbaje, zai zama babbar illa ga ‘yan Najeriya da dimokuradiyyar Najeriya, idan majalissun kasa suka hana INEC tura sakamakon zabe ta hanyar na’ura.

Ya ce, “Hukumar ba ta tsoron yada sakamakon zabe ta hanyar na’ura. A gaskiya, muna da karfin yin hakan. Majalisar ce kawai muke so kada ta ta shiga aikin mu. Kamar yadda muke a yau, na yi imanin cewa hukumar tana da isasshiyar hujja ta doka da za ta tallafa mata don yin hakan.

“Mutane suna ta cewa babu wata doka da ta goyi bayan wannan, amma muna da doka. Abin takaici, wannan doka da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sa wa hannu ba a fitar da ita ba kafin babban zaben 2015, amma an sanya mata hannu kafin zaben.”

Agbaje, ya koka kan karancin halartar masu jefa kuri’a a makwannin farko na ci gaba da rijistar masu jefa kuri’a a jihar.

Comments
Loading...