For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Buɗe Bikin Nuna Fina-Finai Na Duniya A Saudiyya

Za a buɗe bikin fina-finai na farko a ƙasar Saudiyya a birnin Jeddah – kasa da shekaru hudu da ɗage haramcin nuna fina-finai a ƙasar.

Bikin fina-finai a ƙasar zai gudana ne na tsawon kwanaki 10 inda za nuna fina-finai138 daga sassan duniya.

Za a karrama darakta mace ta farko a Saudiyya Haifa al-Mansour – wacce ta fara fim din Wadjda da ta lashe kyauta.

Manufar bikin ita ce bunƙasa masana’antar fina-finai a ƙasar Saudiyya – ta fuskar shirya fina-finai da kuma kasuwarsu da nunawa a sinima da aka buɗe tun shekarar 2018.

Daga: BBC Hausa

Comments
Loading...