For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Bude Makabartun Abuja Bayan Ma’aikatan Muhalli Na Birnin Sun Janye Yajin Aiki

Ma’aikatan Ma’aikatar Kare Muhalli ta Abuja sun janye yajin aikin da suke yi.

Ma’aikatan sun kuma bude makabartu mallakar gwamnati bayan a da sun rufe su da nufin takurawa gwamnatin domin ta biya musu bukatunsu.

A dai ranar Talatar da ta gabata ne, ma’aikatan suka shiga yajin aikin gargadi saboda kin aiwatar musu da sabon tsarin albashi da gwamnatin Abuja ta yi.

Kafin su fara yajin aikin, ma’aikatan sun ce har wa’adi sun baiwa gwamnatin domin ta magance matsalar amma hakan bai haifar da da mai ido ba.

A wata tattaunawa ta waya da jaridar PUNCH, shugaban kungiyar ma’aikatan Muktar Bala ya ce, yan kungiyar sun bude makabartun ne bisa alkawarin da gwamnatin ta yi na duba bukatunsu.

Ya kara da cewa, a kan hakan ne kuma, yan kungiyar suka janye yajin aikin da suka fara domin baiwa gwamnati damar aiwatar da abun da ya kamata.

Comments
Loading...