Bayan gaza samun nasara a ko wasa daya cikin wasanni ukun da Ghana tai a zagayen farko na cin kofin Africa, a jiya Talata an yi waje road da kasar.
Wannan shine karo na farko a tarihin Ghana da bata samu nasara a wasa koda guda daya ba a gasar.
A Jiya, kasar Ghana ta kara wasanta ne da Comoros inda ta sha kashi daci 2 da 3.
A baya dai kasar Ghana ta lashe gasar har sau hudu inda take a mataki na uku na wadanda suka fi kowa yawan lashe gasar ta AFCON.