Wata Babbar Kotu a Abuja ta dage sauraren shari’ar da take yiwa jagoran ‘yan kungiyar IPOB masu neman kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.
A yau ne dai aka tsara ci gaba da saurararen karar wadda aka dage a baya musamman saboda gazawar gwamnatin Najeriya na gabatar da Kanu a kotun.
A wannan karon, an kai Kanu kotun cikin rakiyar jami’an tsaro wadanda suka hana ‘yan jarida daukar bayanai da kuma hotunansa.
An dai dage sauraren karar Kanu zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba na shekarar da muke ciki.
Alkalin da ya saurari karar ya ki amincewa da bukatar da lauyoyin Kanu suka bukata ta a dauke shi daga hannun jai’an DSS zuwa gidan yari.