For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Dage Zaben Shugabannin APC Na Kasa Daga Watan Fabarairu

Jam’iyyar All Progressives Congress, APC mai mulkin Najeriya ta dage Babban Taron Zaben Shugabanninta na Kasa daga watan Fabarairu zuwa watan Yuni.

KU KARANTA: Wasu ‘Yan APC Na Neman Kotu Ta Dakatar Da Taron Jam’iyyar Na Kasa

An gano cewa, yawan kararraki da ke kotuna kan jam’iyyar APC tun daga matakan mazabu, kananan hukumomi, da jihohi da ma rabuwar kan da aka samu a wasu jihohin ne ya sa kwamitin riko na jam’iyyar ya dage Babban Taron.

Daga: NigerianTracker

Comments
Loading...