An shiga halin rashin tabbas a Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa da ke Kaduna a lokacin da ƴan bidiga da sojoji suka yi musayar wuta a kusa da filin a yau Asabar da rana.
Al’amarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na rana, kamar yanda majiyoyi suka baiyana, abun da ya jawo rufe filin jirgin saman na wani lokaci.
Jaridar DAILY TRUST ta gano cewa, jirgin AZMAN wanda aka shirya zai tashi zuwa Lagos na shirin tashi a lokacin da abun ya faru.
Akwai rahotannin da ke cewa, wani ma’aikacin Nigerian Airspace Management Agency (NAMA) ya rasa ransa, yayin da wasu majiyoyin ke musanta hakan.
Akwai karancin sahihan bayanai kan lamarin a lokacin da ake hada wannan rahoton.
Wata majiya da ke aiki a filin jirgin saman ta ce, ba a kaiwa kowanne jirgi hari yayin musayar wutar ba.
Majiyar ta kuma ce, jirgin da ke shirin tashi a wannan lokacin, bai samu damar tashi ba saboda kasancewar ƴan bidiga a kusa da filin jirgin.
An rawaito cewa an tura jami’an sojoji zuwa filin jirgin domin tabbatar da samar da cikakken tsaro.
Kiran wayar da akaiwa Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed bai samu amsuwa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
(DAILY TRUST)