
Wata sanarwa da gwamnatin Gambia ta fitar, ta ce an yi nasarar dakile wani yunkuri da wasu marasa kishin kasa, suka yi na kifar da gwamnatin.
An kama sojoji da dama da wasu mutane uku da ake zargin da hannu a kitsa juyin mulkin sun tsere, amma har yanzu ana ci gaba da nemansu.
BBC Hausa ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne, tun a ranar Talata, kuma kawo yanzu babu cikakken bayani kan wadanda suke da hannu a yunkurin kifar da shugaba Adama Barrow daga mulkin da ya ke kan wa’adi na biyu da aka sake rantsar da shi a bara.
Kasar Gambia na daga cikin kasashen Afirka masu zaman lafiya, da ‘yan yawon bude ido ke yawan zuwa lokutan hutu saboda manyan tekuna da namun daji da ta ke da su.
Shugaba Barrow ya yi nasara a zaben da aka yi na watan Disambar 2016, da shugaba Yahya Jameh ya sha kaye.
An tilastawa Mr Jammeh tserewa daga kasar zuwa Equatorial Guinea, ko da ya ke har yanzu ya na da karfin fada aji a kasar Gambia.