Ana zargin wani ma’aikaci dan shekara 35 mai suna Chris Iruonagbe da satar kwalayen taliya har guda 426 mallakin kamfanin da yake yiwa aiki.
An kai Chris ne gaban Babban Alkalin Majistare, L.O. Owolabi da ke zama a kotun Majistare ta Ogba a Ogba da ke Jihar Lagos, kan zarge-zarge guda biyu da suka hada da hada baki da kuma yin sata.
Ana zargin cewa, wanda ake zargin ya haɗa kai da wasu ma’aikata da suka gudu daga kamfanin, wajen satar taliyar da kudinta ya kai naira miliyan 3 da rabi.
Wadanda ake zargin, sun aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Nuwamban da ya gabata, a kan titin Regina Coker da ke yankin Ikeja a jihar.
Tuhumar da kutun ta yi ta ce, “Kai, Chris Iruonagbe da wadansu da suka gudu, a ranar 22 ga Nuwamba, 2022, da misalin karfe 11:30 na dare, a Ikeja, gurin da ke karkashin hurumin wannan kotu ta majistare, kun hada baki a tsakaninku, kun saci katan din taliya 426 mallakin GPC Energy and Logistics Limited a gini mai lamba 4B, Regina Coker Street, Titin Ajao, Ikeja, Lagos.”
Laifin dai na karkashin hukuncin da ke sashi na 411 da sashi na 287 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Lagos.
Wanda ake zargin dai ya musanta aikata laifin, sannan kuma an bayar da belinsa a kan kudi naira 500,000 da kuma shuwati guda biyu.
Alkalin Majistare, Owolabi, ya dage zaman shari’ar har sai ranakun 16, 17, 18 da 19 ga watan Janairu, 2023.
Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
An Damƙe Wani Ma’aikaci Saboda Satar Kwalin Taliya 426
Comments