For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Daure Wani Mai Ikirarin Shi Karuwa Ce ‘Yar Amurka, Watanni 12 Saboda Damfara Ta Naira Miliyan 57.8

Alkali Mahmud Abdulgafar na Babban Kotun Jihar Kwara da zamanta a Ilorin, ya yanke hukuncin daurin watanni 12 a ranar Juma’a ga dan shekara 20, Fawas Oyelowo kan laifuffukan da suka shafi yanar gizo.

Wanda aka yankewa hukuncin wanda ya fito daga karamar hukumar Atiba da ke jihar Oyo, an yanke masa hukunci rubi biyu ne wadanda Ofishin Yanki na Hukumar Yaki da Cin Hanci Rashawa, EFCC tai kararsa a kai.

Baya da ikirare-ikirare da dama, Fawas, ya yi karyar cewa shi farar mace ce kuma kwararriyar karuwa mai karuwanci a kasar Amurka.

Hukuncin ya ce “Kai, Oyelowo Mayowa Fawas, wani lokaci a watan Yuni na shekarar 2020 da watan Yuni na shekarar 2021 a garin Ilorin na jihar Kwara, a karkashin kulawar wannan kotu, kana sane ka mallaki kudi naira 57,837,710 wanda aka sanya a asusun bankinka na Bankin Access mai lamba 0804708906, wanda akai zargin ka mallakesu ta hanyar da ba ta dace ba, hakan ya sa ka aikata laifi kamar yanda yake kuma akai tanada masa hukunci a Sashi na 319A na Kundin Laifuffuka.”

Wanda ake zargin ya masa laifuffukan da ake zarginsa a kai wadanda aka karanta masa.

Ikirarin wanda aka kama, wayoyin iPhones da kwamfiyuta laptop da aka samu a wajen wanda ake zargin sun zame shaidun da kotu tai amfani da su.

A hukuncin da Alkali Abdulgafar ya gabatar, ya kama Fawas da laifuffuka biyu, inda ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida a kan kowanne laifi tare da tarar naira dubu dari akan kowanne laifi.

(PUNCH)

Comments
Loading...