Rahotanni daga jihar Zamfara sun ce an gano gawarwakin mutane fiye da 140, wadanda ‘yan bindiga suka kashe yayin munanan hare-haren da suka kai kan wasu kauyukan kananan hukumomin Bukuyyum da Anka a tsakanin ranakun Laraba da Alhamis da suka gabata.
Wasu majiyoyi sun ce, daruruwan ‘yan ta’addan da suka kaddamar da munanan hare-haren, masu biyayya ne da kasurgumin dan fashin dajin nan Bello Turji, wadanda hare-haren jiragen yakin sojin Najeriya ya tilastawa tserewa daga sansanoninsu da ke dajin Fakai a karamar hukumar Shinkafi.
KU KARANTA: Helkwatar Tsaro Ta Ce An Kashe ‘Yan Ta’adda 950 Da ‘Yan Bindiga 537 Cikin Watanni Bakwai
Wani mazaunin yankin da ya shaida aukuwar lamarin, ya shaidawa jaridar Daily Trust da ke Najeriya cewar, ‘yan ta’addan sun rika budewa mutane ciki har da mata da kananan yara wuta da miyagun bindigogi da zarar sun yi yunkurin tserewa daga gidajensu da maharan suka cinnawa wuta.
Haka zalika adadin kauyukan da ‘yan bindigar suka afkawa ya kai akalla 10, sabanin 6 da akasarin kafofin yada labarai suka ruwaito.
Sai dai har yanzu babu karin bayani kan alkaluman wadanda wannan tashin hankali ya rutsa da su daga bangaren hukuma.
Daga: RFI Hausa