For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Harbe Ƴan Shi’a 6, Yayinda Da Dama Suka Sami Raunuka A Zaria

Mambobin ƙungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) waɗanda aka fi sani da ƴan Shi’a da ba su gaza 6 ba ne aka rawaito an kashe yayinda waɗanda ba a tantance ba suka tsira da munanan raunuka a lokacin da suke yin muzaharar ranar Ashura a jiya a Zaria.

Da yake tabbatar da mutuwar ga jaridar THE NATION, shugaban ƙungiyar a Zaria, Malam Abdulhamid Bello ya zargi haɗakar jami’an tsaro da yi musu kutse cikin muzahararsu a daidai kasuwar birnin Zaria, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi, abun da ya jawo mutuwar mambobinsu yayinda wasu da dama suka sami raunuka.

Ya faɗi sunayen waɗanda aka kashe musu da suka haɗa da Jafar Magaji Jushi, Kazeem Lawal Magume, Ali Lawal Samaru, Muhsin Badamasi Yakub Zakzaky, Umar Inuwa Anguwar Fatika da wani guda ɗaya da bai iya tuna sunansa ba.

Bello ya bayyana cewa ba a gama tantance adadin waɗanda suka ji raunuka ba, sai dai ya ƙara da cewa, an kai da damansu asibitin St Luke da ke Wusasa yayinda aka kai waɗanda suka sha wahala sosai asibitin koyarwa na ABU da Shika a Zaria.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalinge ya ce, yana sane da faruwar lamarin amma har yanzu ba ai masa cikakken bayani game da ainihin abun da ya faru ba.

Comments
Loading...