A harin da ƴanbindiga suka kai Ƙaramar Hukumar Ajaokuta ta Jihar Kogi a ranar Juma’a da daddare, sun kashe ƴansanda aƙalla 2 tare da yin garkuwa da wasu Indiyawa 14.
Da take mayar da martani kan harin, gwamnatin Jihar Kogi ta ce tana aiki da tuƙuru tare da jami’an tsaro domin kuɓutar da waɗanda akai garkuwa da su.
Mai magana da yawun ƴansandan jihar, William Ovye Aya ya ce, tsaron jihar ya taɓu inda ƴanbindiga suke kai hari kan al’ummu da dama a jihar.
Ya bayyana cewa, duk lokacin da suka yi ƙoƙari wajen aiwatar da dabarun samar da tsaro a jihar, sun gano cewa akwai masu yi musu zagon ƙasa.
Ya ce abun da ya kamata a yi a irin wannan yanayi shine a bi ƴan ta’addar a kamo su a gurfanar da su a gaban shari’a.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar, haɗin gwiwa da jami’an tsaro da kuma ƴan bijilanti na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kuɓuto da waɗanda akai garkuwa da su cikin salama.
A ƙarshe ya kuma yi kira ga al’ummar Ajaokuta da su ci gaba da al’amuransu yanda ya kamata, inda ya ce gwamnati ta tanadi duk wani shiri na kare su.