For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Harbe Wani Mai Temakawa Sanata Har Lahira

Adeniyi Sanni da ke a matsayin babban mai temakawa sanatan Ogun ta Yamma, Solomon Adeola ya gamu da ajalinsa bayan harbinsa da akai lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa gidansa da ke yankin Isheri a Jihar Lagos jiya Asabar.

A wani jawabin da aka bayar jiya a Abuja, mai magana da yawun Sanata Solomon, Kayode Odunaro, ya ce, an tsinci gawar marigayin ne da raunukan harbin bindiga a tashar Toyota da ke yankin Oshodi a Jihar Lagos a jiya Asabar da safe.

Ya ƙara da cewa, Adeniyi ya kira matarsa yana tambayarta bayanai kan takardun motarsa, daidai lokacin da jami’an tsaro suka tsare shi a wajen binciken ababen hawa da ke yankin Berger a jihar.

Ya ce, matar ta shiga ruɗani lokacin da ta gaza samunsa a waya bayan ta tura masa hotunan takardun motar ta WhatsApp.

Daga baya ne matar ta kira abokan Adeniyi ta sanar da su cewar ta kasa samun mijinta a waya, abin da ya sa aka tura masu bincike.

Bayan haka, sai wasu masu wucewa suka kirata ta hanyar ɗaukar lambar wayar ɗan-uwa da ke jikin katin tuƙinsa suka sanar da ita cewar, an jefar da gawar mijinta a wajen tashar Toyota a Oshodi bayan an harbe shi.

Kayode ya ƙara da cewa, Sanata Solomon Adeola wanda ke cikin zauren Majalissar Dattawa wajen tantance ministoci, ya matuƙar kaɗuwa da jin mummunan labarin, saboda Adeniyi makusancinsa ne sosai na tsawon sama da shekaru ashirin.

Comments
Loading...