Daga: Haruna Ahmad Bultuwa
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da Majalissun Gudanarwar sabbin kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi guda takwas a kasar nan.
Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya gudanar da aikin ta hannun Karamin Ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba a ranar Talata.
Ministan yace an zabo mambobin ne majalissun ne dai-dai da yadda doka ta shekarar 2019 ta kwalejojin ilimi ta tarayya ta tanada.
“Ana sa ran wadanda aka zaba don zama shugaban ko kuma su zama mambobin majalissu daban-daban za su kasance ƙwararrun maza da mata da suka tabbatar da gaskiya, waɗanda ba wai kawai ƙwararrun masana kimiyyar kere-kere da kwalejojin harkokin ilimi ba ne, har ma suna da masaniyar zaɓin manufofin gwamnati a Nijeriya, da tsarin ilimi na jami’a,” a cewar Minister.
KU KARANTA: Khadija University Majia Ta Yi Ragi Na Musamman Ga Daliban Jigawa Da Kano
Don haka, ina taya ku murna da kuka yi tsayuwar daka wajen tantancewa kuma aka gano kun cancanci nadin da kuka yi,” in ji shi.
A cewarsa, “A cikin tsarin ilimi na ma’aikatar ɗaya daga cikin dabarun magance matsaloli da ƙalubalen ilimi na manyan makarantu, shi ne naɗin shugabanni da membobin majalisar gudanarwa daga cikin mutanen da suka tabbatar da gaskiya da gogewa a fannin Ilimi da gudanarwa”
Ya kuma kara da cewa “A saboda haka ne muka nemi ƙwararrun ƴan Najeriya da za su taimaka wajen cimma manufofin ilimi na ƙasarmu. Yunkurin sake fasalin ingantaccen ilimi na manyan makarantu a Najeriya ya rataya ne a wuyan fitattun ‘yan kasa irinku”.
“Muna da yakinin cewa za ku kawo arziƙinku na gogewarku, riƙon amana da mutunta doka da bin tsarin da ya dace don aiwatar da ayyukanku” inji Ministan Ilimin.