For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Kama Malamar Makaranta Saboda Bulale Dalibi Dan Shekara 2

Wata malamar makaranta da ake kira da Joy, ta shiga hannun ‘yansanda bayan an zarge ta da zane dalibi dan shekara 2 na makarantar Unic Vilos School, Mazamaza da ke Jihar Lagos.

An kama ta ne a ranar Litinin bayan ayarin jami’an magance matsalolin rikicin gidaje bangaren ingancin ilimi da aiyukan al’umma sun ziyarci makarantar domin binciken abun da ya faru ga dalibin.

Wadannan jami’ai sun samu masaniya kan faruwar abun ne, bayan an wallafa rubutu a dandalin Twitter kan batun a shafin wakawakatailor a makon da ya gabata.

Mahaifiyar dalibin, Faustina Ohamadike, ta fadawa jaridar The Nation cewa, malamin ya zane dalibin ne bulala 24 da tsumagiya saboda ya kasa karanta haruffan Turanci.

An baiyana cewa, binciken farko ya nuna cewa an yi dukan, yayin da aka mika batun zuwa ga ‘yansanda.

Tuni dai an kai yaron asibitin Amuwo Odofin General Hospital saboda a kula da lafiyarsa.

(THE NATION)

Comments
Loading...