For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Kama Malamin Jami’a Saboda Bukatar Yin Lalata Da Karbar Kudi A Wajen Daliba Don Ba Ta Maki

Hukumar Yaki Da Almundahana Da Saba Ka’idojin Aiki, ICPC, ta kama wani mai suna Dr. Balogun Olaniran, malami a Tai Solarin University of Education, (TASUED) da ke Ijebu-Ode, Jihar Ogun, bisa zargin cin zarafin daliba da neman kudi a wajenta.

An gurfanar da Olaniran a gaban Justice Osinuga na Babbar Kotun Ijebu-Ode da ke zamanta Ijebu-Ode kan zargin sabawa Sashi na 8(1) (a) na Dokar ICPC ta shekarar 2000.

Lauyan ICPC ya fadawa kotun cewa, Olaniran, a matsayinsa na Shugaban Sashin Nazarin Addini a TASUED, a wani lokaci cikin watan October da November na 2021 ya bukaci yin lalata ko karbar kudi naira 100,000 daga daliba da alkawarin gyara mata makin jarabawarta.

To sai dai kuma, wanda ake zargin ya musanta aikata laifin lokacin da aka tuhume shi, yayin da alkalin da ke sauraron karar ya bayar da belinsa a kan kudi naira 500,000 da kuma mai tsaya masa.

Justice Osinuga ya kuma bukaci mai tsayawa wanda ake zargin da ya gabatar da shaidar biyan haraji ta shekara 3 da kuma hanyar samun kudaden biyan harajin.

Alkalin ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan May, 2023 domin fara karbar shaidu.

Comments
Loading...