Masu temakawa ‘yan ta’adda sama da 2000 ne aka kama a jihar Zamfara sakamakon katse layin sadarwar da aka yi a jihar, a cewar Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai, Al’adu da Yawon shakatawa na jihar, Alhaji Ibrahim Dosara.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis din nan yayin da yake ba da bayanai kan ayyukan sojoji da ke gudana a jihar.
Ya ce wadanda ake zargin na fuskantar tsauraran tambayoyi domin su bayyana sauran wadanda ke aikata laifin da kuma abokan aikin su.
A cewarsa, wasu daga cikin wadanda aka kama sun ambaci sunayen manyan mutane masu tasiri a matsayin abokan aikin su.
Ya ce hukumomin tsaro suna aiki kan bayanan da suka bayar don kamo wadancan abokan aikin.
Dosara ya ce jami’an tsaro da ke aiki a fadin jihar sun kashe ‘yan bindiga da yawa yayinda da yawa suka tsere zuwa makwabtan jihohi kamar jihohin Sokoto da Katsina.
“Mun samu nasarori masu yawa a cikin wata guda da ya gabata na aikin yayin da ‘yan bindiga da yawa suka tsere daga jihar zuwa Sokoto da jihar Kastsina. Mun yi nasara da yawa ta hanyar sanya da yawa daga cikinsu su tsere daga Jihar.
“Kwana daya da ya gabata Kwamishinan‘ yan sanda a Sakkwato ya ce kashi 80 na barayin Zamfara yanzu suna Sokoto yayin da kashi 20 kacal suka rage a Katsina da Zamfara. Kamar yadda a yanzu hukumomin tsaro suka cafke sama da mutane 2000 masu ba da labarai ga masu laifi a jihar kuma ana ci gaba da yi musu tambayoyi sannan sun ambaci sunayen abokan aikin nasu ciki har da wasu manyan mutane. Hukumomin tsaro kuma suna aiki kan bayanan da aka bayar don kamo abokan huldarsu,” in ji shi.