Hukumar kula da shige da fice, reshen jihar Oyo ta ce ta kama ta kuma fitar da ‘yan kasashen waje 18 saboda mallakar katin zabe.
Shugaban hukumar a jihar, Isah Dansuleiman, ne ya bayyana haka a lokacin taron wayarwa da masu ruwa da tsaki kai game da zabukan da za a yi na 2023, a jiya Laraba.
Taken shirin shi ne: ”Zabe mai inganci a Najeriya : Abin da ake tsammani daga baki kafin lokacin da kuma bayan zabe.”
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito, shugaban na bayanin cewa, sun kama bakin ne a lokacin farmakin da suka kai a sassan jihar ta Oyo.
Ya ce, kasancewar bakin sun saba dokokin Najeriya a don haka aka fitar da su zuwa kasashensu.
Ya yi gargadin cewa ba wani bako komai matsayinsa a Najeriya da zai yi zaben, kuma duk wanda aka kama da katin zaben zai fuskanci hukunci.
Ya bukaci baki a jihar su zauna tare da gudabar da harkokinsu bisa doka idan har suna da takardun zama, amma kada su kuskura su shiga harkar zabe.