‘Yansandan Najeriya sun sanar da kara wa’adin karbar bayanan masu neman aikin dansanda wanda ake diba na shekarar 2021.
Masu sha’awar neman aikin dansanda a matakin constables yanzu suna da damar nemar aikin har zuwa nan da ranar Asabar 22 ga watan Janairu na 2022.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansanda, Frank Mba ya fitar, ya ce shafin cike neman aikin zai kasance a bude har zuwa daren sabuwar ranar da aka saka.
Mba ya ce, karin wa’adin ya samu ne domin a samu karin masu neman aikin, musamman domin yankin Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da kuma jihar Lagos su cika adadin abun da aka warewa yankunansu.
KU KARANTA: An Saki Sunayen Wadanda Suka Sami Aikin ‘Yan Sanda
‘Yansandan sun bayyana cewa adadin mutane 81,005 suka cike neman aikin a duk fadin kasar kawo ranar 7 ga Janairu na 2022.
“Iya mutane 1,404 ne kawai suka nemi aikin daga jihohi 5 na yankin Kudu maso Gabas, yayin da mutane 261 aka samu daga jihar Lagos, jihar Anambra kuma ita ce ta fi kowacce jiha karancin masu neman inda take da masu nema 158”, in ji Mba.
Ya yi kira ga jihohi, kananan hukumomi, addinai da sauran masu ruwa da tsaki a yankunan da abun ya shafa da jihar Lagos da su zaburar da wadanda suka cancanta domin su nemi aikin.
“Ana kira ga wadanda suke sha’awar aikin da su shiga shafin daukar aikin ‘yansanda www.policerecruitment.gov.ng domin su yi rijista kafin karewar wa’adin.”
Masu neman aikin za su iya kiran 08100004507 domin neman karin bayani ko mika korafi kan matsalar na’ura yayin anfani da shafin.