For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Kashe Mutane Da Dama A Harin Da Aka Kai Coci A Ondo

Sama da mutane 40 ne aka kashe a harin da aka kai kan Cocin St Francis Catholic, da ke Titin Owa-luwa, a garin Owo na Ƙaramar Hukumar Owo ta Jihar Ondo.

An gano cewar, al’amarin ya faru a cocin ne, wadda ke ƙasa da mita 200 zuwa Fadar Olowo na Owo.

Ma’aikata da ke aiki a asibitin Federal Medical Centre, Owo, sun tabbatar da cewa, an kawo musu mamata da dama a yau Lahadi.

An dai kai harin ne lokacin da ake cikin ibadar ranar Lahadi.

Wani bidiyo da ake ta yaɗawa a yanar gizo, ya nuna wasu masu ibada a mace a kwance a cikin cocin cikin jini.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan da ke kan aiki a asibitin Federal Medical Centre, Owo, inda aka kai waɗanda abin ya rutsa da su, ya ce, an kai sama da mutane 50 zuwa asibitin.

Ya ce, “Har yanzu suna kawo mutane zuwa asibitin, waɗansu an riga an tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu kuma suna nunfashi. Amma a yanzu haka ba zan iya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba.”

Da take tabbatar da faruwar lamarin, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansanda, Mrs Funmilayo Odunlami, ta ce, har yanzu rundunar ƴansanda ba ta tantance abin da ya jawo faruwa lamarin ba.

“CP (Kwamishinan Ƴansanda) na kan hanyarsa ta zuwa inda abin ya faru domin ya tabbatar da abin da ya jawo faruwar lamarin. Mun ji ana cewa abubuwa da dama game da lamarin, amma dai zamu waiwaice ku,” in ji ta.

Comments
Loading...