For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Kashe Sarki Da Dogarai An Kone Gawarsu A Jihar Ogun

Wasu ‘yan bindiga da ba a sansu ba sun kashe basaraken gargajiya na kauyen Agodo da ke karamar hukumar Ewekoro a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, inda kuma suka kona shi tare da dogarawansa kurmus.

Rahotanni sun ce maharan sun kashe tare da kone Kabiesi Oba Odetola da dogaransa hudu, jim kadan da shigar basaraken da tawagarsa garin da kusan karfe goma sha daya na safiyar jiya Litinin 24 ga watan Janairun 2022.

Bayanai na nuna cewa wannan shi ne karo na biyu da irin wannan abin takaici ya auku a garin cikin ‘yan watannin nan.

KU KARANTA: Ganduje Ya Yi Alwashin Amincewa Da Hukuncin Kisa Ga Wadanda Sukaiwa Hanifa Ta’addanci

Rikici ya fara ne a garin tun bayan da aka nada marigayin sarkin, wanda aka ce ya fito ne daga wata haular ta daban ta Ake a matsayin sarkin garin, amma kuma al’ummar garin, ‘yan Owu aka ce sun kafe cewa ba ta yadda za a nada musu sarki daga cikin al’ummar Ake ya mulke su.

Da take tabbatar da abin da ya faru daya daga cikin ‘yan uwan marigayin, Chief (Mrs) Adenike Akintade, ta nuna takaicinta kan yadda ta ce mutanen sun nuna tsabar rashin imani da tausayi suka kashe sarkin da dogaransa, inda ta kara da cewa a baya-bayan nan ma mutanen sun hallaka kanin marigayin ta hanyar daddatsa shi.

Kakakin ‘yan-sanda na jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma kuma ya musanta maganar kashe dogaran sarkin.

Ya ce zuwa yanzu ba wanda aka kama amma kuma jami’ai sun shiga farautar wadanda suka aikata laifin.

(BBC Hausa)

Comments
Loading...