For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Kashe Sojoji 10 Yayin Da Ƴan Bindiga Suka Kai Hari Sassanin Sojoji A Kaduna

A kalla sojoji 10 ne aka rawaito sun mutu yayinda waɗansu kuma suka ji raunuka daga harin ƴan ta’adda wanda suka kai a sassanin sojoji da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Al’amarin ya faru ne jiya Litinin da yamma da misalin karfe 6:30 kamar yadda majiyoyi suka baiyanawa gidan talabijin na CHANNELS.

Sai dai kuma, hukumomin sojojin har kawo yanzu ba su tabbatar da harin ba.

Birnin Gwari na daya daga cikin guraren da ƴan ta’adda ke addaba a Kaduna, inda aka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu da kuma lalata ci gaban tattalin arzikin wasu cikin shekaru biyar da suka gabata.

Wata majiyar tsaro a yankin ta sanar da CHANNELS a yau Talata cewa, an kaiwa sojojin hari ne a sansaninsu da ke yankin Polwire kusa da gonar Mikati Farm da ke kan titin Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Hoton sojojin da aka kashe | CHANNELS

Majiyar ta baiyana cewa, sojojin waɗanda ba su da yawa, an fi karfinsu ne bayan da ƴan ta’adda da dama suka shigo sansanin a kan babura da manyan makamai tare kuma da budewa sojojin wuta.

Majiyar ta kara da cewa, ƴan ta’addar sun faki sojojin ne ta yanda sai da suka lura ba su da yawa suka afka musu.

Afkawar ƴan ta’addar dai ta yi sanadiyyar mutuwar sojoji 10, yayin da kuma aka lalata wata motar ajjiye man fetur yayin harin.

(CHANNELS)

Comments
Loading...