Kusan Sojoji 750 ne suka rasa rayukansu a tsakanin watanni ukun ƙarshen shekarar 2020 zuwa watan Yuli na shekarar nan ta 2022.
Jaridar PUNCH ta rawaito a watan Afrilu cewa, sojojin da ba su gaza 714 aka kashe kawo wannan lokacin.
Bincike ya nuna cewa a tsakanin watan Mayu da watan Yuli na shekarar 2022, an kashe sojoji 35, abun da wasu tsofin manyan sojoji suka bayyana a matsayin gagarumin ci bayan da ba za a yarda da shi ba.
Alal misali, sojoji shida na bataliya ta 93 da ke Takun, an kashe su a ranar 10 ga watan Mayu lokacin da ƴan ta’addar suka farmaki jerin gwanon motocin da ke rakiya ga kwamandan bataliyar a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Jalingo babban birnin Jihar Taraba.
Haka kuma, sojoji 20 ne ƴan ta’adda suka kashe a yayin harin da suka kai kan kamfanin haƙar ma’adanai da ke Ajata-Aboki a mazaɓar Gurmana ta Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Niger a ranar 30 ga watan Yuni na 2022.
Ɓatagarin kuma sun ƙara farmakar wasu manyan sojoji na 7 Guards Battalion of the Nigerian Army Presidential Guards Brigade, a ranar 22 ga watan Yuli inda suka kashe sojoji takwas ciki har da mai muƙamin kaftin da kuma lieutenant.
An kuma rawaito cewa, harin da aka kai kan wajen binciken ababan hawa a Zuma Rock a ranar 28 ga watan Yuli ya yi sanadiyar mutuwar soja guda ɗaya yayin da kuma wasu sojojin guda biyu suka tsira da raunuka bayan fafatawa da ƴan ta’addar.