Yau Jumma’a, aka bude taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 a tsibirin Bali na kasar Indonesiya. Taken taron shi ne “Hada kai don gina duniya mai zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata”.
Tun daga ranar 7 ga wata, ministocin harkokin wajen kasashen G20 suka fara shawarwari a tsakaninsu, daya bayan daya.
Kasashen G20 a wannan shekarar ta 2022 sune: Argentina, Australia, Brazil, Canada, China, France, Germany, India, Indonesia, Italy, South Korea, Japan, Mexico, Russia, Saudi Arabia, South Africa, Turkey, Birtaniya, Amurka, da Kungiyar Tarayyar Turai.