Shugaban Jami’ar Abuja, Farfesa Abdulrasheed Na’Allah ya ce, jami’ar ta kori malamanta guda biyu saboda zarginsu da aikata baɗala a kwanan nan.
Shugaban ya kuma faɗawa wakilin jaridar PUNCH cewa, jami’ar ta tsara wata kafa ta musamman da ɗalibai zasu amfani da ita wajen fallasa yunƙurin baɗala ko aikata wani aikin assha daga ɓangaren malamai.
Ana dai yawan samun rahotanni kan aiyukan baɗala a manyan makarantun Najeriya, inda rahoton da Bankin Duniya reshen harkokin mata ya fitar a shekarar 2018 ya nuna cewa kaso 70 cikin 100 na ƴan matan da suka kammala digiri a Najeriya sun fuskanci yunƙurin aikata baɗala da su.
Rahoton ya nuna cewa, waɗanda ke yiwa ƴan matan wannan barazana, ƴan ajinsu ne da kuma malamansu.
To sai dai kuma, duk da ƙudirin dokar da Majalissar Dattawa ta amince da shi a shekarar 2021 wanda ya tanadi hukuncin ɗaurin shekaru 21 ga duk malamin da aka kama da wannan laifi, rahotanni sun nuna cewa, malaman da aka kama da laifin bayan dokar sun samu hukuncin kora da aiki ne kawai.
A shekarar 2022, jaridar PUNCH ta rawaito cewa jami’o’in UNIABUJA, Jami’ar Obafemi Awolowa da wasu manyan makarantun sun kori aƙalla farfesoshi huɗu da wasu malaman 14 a matakai daban-daban bisa zarginsu da aikata baɗala.
