For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Kulle Lauyan Sarki Sanusi A Kano Bayan Kotu Ta Yanke Hukuncin Da Baiwa Gwamnati Dadi Ba

Bayan awanni 24 da wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta umarci gwamnatin jihar Kano da ta nemi gafarar tubabben sarkin Kano, Sunusi Lamido Sanusi, sannan ta biya tsohon sarkin  kudi naira miliyan 10 bisa laifin take masa hakkinsa, an kulle lauyansa, Nureni Jimoh a ranar Laraba a cikin ofishinsa da ke Kano.

Da aka tuntube shi ta wayar tarho domin jin ta bakinsa game da faruwar lamarin a ranar Larabar, Jimoh ya ce an kulle shi kuma ba zai iya fitowa daga ofishinsa ba, yana mai cewa ya samu damar sanar da Daraktan Tsaron Jihar.

Wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta a safiyar ranar Larabar ta ce, yanzu haka an fara mayar da martani ga hukuncin da aka yanke kan mulkin jam’iyyar APC wanda ya saba da muradin Gwamna Abdullahi Ganduje da kuma hukuncin na Sarki Sanusi.

Majiyar ta ce “Nureni Jimoh, wanda shine jagora a shari’ar da akai da APC kuma jigo a bangaren lauyoyin Sarki Sanusi, gwamnatin jihar Kano ta kai masa hari.”

Bugu da kari, majiyar ta bayyana cewa, “Tawagar ‘yan sanda da wasu ma’aikatan Ma’aikatar Kasa ta jihar Kano sun afkawa ofishin lauyan tare da kulle shi a ciki da wani makulli.”

Haka kuma, kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar da ma’aikatar kasa ya ci tura, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

A lokacin da wakilin PUNCH ya ziyarci ofishin Jimoh da ke lamba 16, Murtala Muhammad Way, an cire hatimin da aka sanya a kofar shiga babban ginin.

Wani jami’in ma’aikatar filaye ya shaida wa manema labarai cewa, “Ma’aikatar ta rufe ginin ne bisa umarnin Babban Sakatare.”

Jami’in ya kuma bayyana cewa babban sakataren ya umarce su da su cire tambarin da kuma bude harabar.

Sai dai da yawa daga cikin mazauna ofishin sun ce mutanen da suka zo rufe babban ginin sun zo ne tare da jami’an tsaro masu dauke da makamai.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Haruna Kiyawa, ya ce, “Daga bincike da hirar da aka yi da wasu daga cikin mutanen ofishin, sun ce babu ‘yan sanda daga cikin wadanda suka zo rufe ofishin.”

Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kuma da zarar ‘yan sandan sun kammala bincikensu za a sanar da manema labarai.

Comments
Loading...