Akawun Majalissar Tarayya, Arch. Olatunde Amos Ojo, a yau Litinin ya mikawa Shugaban Kasa daftarin gyaran dokar zabe wanda akaiwa gyara domin ya sanya hannu.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa, wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta tabbatar da cewa yanzu haka kudirin dokar yana gaban Shugaban Kasa.
Da ma a baya, jaridar The Nation ta rawaito cewa, a yau ne za a mikawa Shugaban Kasar kudirin.
A watan Disambar da ya gabata ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ki sanyawa kudirin dokar hannu, abinda ya sa majalissar ta kara yiwa kudirin gyaran fuska.
Har yanzu dai ba a da tabbacin ko shugaban zai sanya hannu a kan dokar a wannan karon.
Wannan kuwa ya biyo bayan rahotanni da ke nuni da cewa, gwamnoni ba sa maraba da gyaran fuskar kuma za su sa shugaban ya ki amincewa.