For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Kenya, William Ruto

Kusan mutum 60,000 ne suka taru a filin wasan Kenya da ke Nairobi, don shaida rantsar da sabon Shugaban kasar William Ruto, wanda ya lashe zaben shugaban kasa a watan jiya.

Akalla mutum takwas ne suka jikkata a turmutsutsin da ya faru wurin shiga filin wasan.

Dan takarar da ya sha kaye Raila Odinga ya sanar cewa ba zai halarci bikin rantsuwar ba saboda shakku da yake da shi game da nasarar abokin hamayyarsa.

Mr Ruto ya lashe zaben ne da kashi 50.5 na kuri’u, yayin da Mr Odinga ya samu kashi 48.8. Mr Odinga ya yi zargin cewa an tabka magudi a zaben, sai dai Kotun Koli ta yi watsi da zargin.

Akalla shugabannin kasashe 20 ne ake sa ran za su shaidi bikin rantsuwar.

Shugaba mai barin gado Uhuru Kenyatta zai bar mulki bayan shafe wa’adi biyu.

Mr Kenyatta, wanda ya goyi bayan Mr Odinga a zaben, ya bayyana cewa Mr Ruto bai cancanci ya zama shugaban kasa ba.

Hakan ya haifar da tsama a tsakanin mutanen biyu, kuma Mr Kenyatta bai taya sabon shugaban murna ba hari sai saura kwana daya a rantsar da shi.

Mr Kenyatta ya ce a shirye yake ya ga cewa ya mika mulki lami lafiya, inda ya yi kira ga sabon shugaban da ya rungumi duka al’ummar Kenya a tafiyarsa.

A sanarwar da Mr Odinga ya fitar, ya ce Mr Ruto ya kira shui a wayar tarho yana gayyatar shi domin ya halarci bikin rantsuwar, amma ya ce ba zai samu zuwa ba don yanzu haka yana kasar waje, kuma ma bai amince da sahihancin zaben ba.

Wannan kuma na zuwa ne duk da cewa Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Mr Ruto tare da watsi da karar Mr Odinga cewa akwai kura-kurai a zaben.

Mr Ruto ya lashe zabe ne bayan ya bayyana kansa a matsayin ”mai neman na kansa”, da ke fuskantar ‘yan zuri’ar masu fada a ji a kasar, wato iyalan gidan Odinga da Kenyatta da ke son ci gaba da kankane madafun iko a kasar.

Ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin Kenya, ta hanyar samar da aikin yi a tsakanin matasa da kuma inganta rayuwar al’umma.

(BBC Hausa)

Comments
Loading...