For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Rike Albashin Ma’aikata 731 a Gombe

Gwamnatin jihar Gombe ta dakatar da biyan albashi ga ma’aikata 731 saboda kama su da aka yi da laifin rashin zuwa wajen aiki a watan Satumba, inda ake gudanar da bincike kan karin wasu guda 170.

Kwamishinan Kudi da ci Gaban Tattalin Arziki na jihar, Malam Muhammad Magaji ne ya bayyana haka a taron manema labarai na wata-wata da aka ikan tantance ma’aikata a Talatar nan.

Kwamishinan ya ce; gwamnatin jihar ta sami nasarar kubutar da Naira Miliyan 57.68 daga dakatar da ma’aikatan da akai.

Ya kuma bayyana cewa, akwai wasu ma’aikatan guda 170 wadanda yawan albashinsu ya kai Naira Miliyan 19.66 da ake yiwa bincike, inda ya karab da cewa, za a biya su albashinsu.

“Za a biya su saboda sun sami halartar wajen aikinsu, sai dai za a binciki dalilin da ya sa suka kasance cikin jerin sunayen.”

“Wadanda aka dakatar daga karbar albashin su 731 ne da albashinsu ya kai Naira 57,682,403. Sai kuma wadanda ake yiwa bincike su 170 da albashinsu ya kai Naira 19,658,080.

Comments
Loading...