An rufe taron kolin Tarayyar Turai, EU, na lokacin hunturu a Brussel, babban birnin kasar Belgium a daren jiya agogon kasar.
Shugaban majalisar zartarwa na EU, Charles Michel, ya bayyana wa manema labarai a gurin taron da aka gudanar, cewa, shugabannin kasashen EU sun amince da shirin kakabawa Rasha takunkumi zagaye na tara.
Haka kuma, a cikin taron kolin a wannan rana, shugabannin kasashen EU sun amince da ba da tallafin tattalin arziki na euro biliyan 18 a hukumance ga kasar Ukraine a shekarar 2023 mai zuwa.
A daidai lokacin kuma, an amince da Bosnia da Herzegovina a matsayin ‘yan takarar neman shiga Tarayyar Turai a hukumance.
CRI Hausa