For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Saka Ranaku, Gurare Da Lokutan Tantance Ƴan J-Teach Masu Digiri A Jigawa

Ma’aikatar Ilimi mai Zurfi, Kimiya da Fasaha ta Jihar Jigawa ta sanar da ranakun tantance waɗanda suka zana jarabawar neman aikin koyarwa na J-Teach a jihar.

Ma’aikatar ilimin ta rarraba ranakun gudanar da tantancewar zuwa yankunan ilimin da ake da su a jihar.

Ga bayanin gurare da ranakun da za ai tantancewar:

Alhamis 17/8/2023 za a yi wa Yankin Gumel da Babura a Gumel.

Juma’a 18/8/2023 za a yi wa Yankin Hadejia da Birniwa  a Hadejia.

Asabar 19/8/2023 za a yi wa Yankin Kazaure da Ringim a Kazaure.

Litinin 21/8/2023 za a yi wa Yankin Jahun da Kafin Hausa a Jahun.

Talata 22/8/2023 za a yi wa Yankin Dutse da Birnin Kudu a Dutse.

A ko wacce rana za ana fara tantancewar ne da misalin ƙarfe 9 na safe, kamar yanda Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi mai Zurfi, Kimiya da Fasaha, Wasilu Umar Ringim ya faɗa.

Comments
Loading...