Rundunar ‘Yan Sanda ta saki sunayen wadanda suka sami aikin dan sanda, ranaku, wuri, da kuma abubuwan da ake bukata domin karbar horo.
Wannan yana kunshe ne cikin sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda reshen jihar Enugu, ASP Daniel Ndukwe ne ya bayyana hakan a Alhamis din nan.
ASP Daniel ya sanar da wadanda suka nemi aikin da su ziyarci shafin daukar aikin ‘yan sanda, www.policerecruitment.gov.ng domin su sami jerin sunayen, ko kuma su ziyarci ofisoshin Rundunar ‘Yan Sanda na jihohinsu domin su duba sunayen.
KU KARANTA: EFCC Ta Samu Nasarar Hukunce-Hukunce 2220 A 2021
“Rundunar ‘Yan Sanda tana farincikin sanar da mazauna wannan jihar cewa, duk wanda ya nemi aikin ‘yan sanda na shekarar 2020 wanda za a debi mutane 10,000, kuma ya je binciken lafiya, cewar sunayen wadanda suka sami nasara ya fito.
“Bayanan wadanda suka samu din yana kunshe da ranar farawa, wuri da kuma abubuwan da ake bukata domin karbar horo.
“Wadanda suka sami nasarar, wadanda suka sami sunayensu sai su je wuraren da aka ware musu a kwalejojin ‘yan sanda domin karbar horon fara aiki.”
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce duk wadanda suka sami aikin, su je kwalejojin ‘yan sandan da kayayyaki kamar fararen T-shirts da gajerun wanduna, da fararen takalma sau ciki, da fararen safa, da fararen sportswears, da fararen zanin gado, da fararen rigunan matashin kai duk guda bibiyu, sannan kuma da face mask da kuma hand sanitizer.
“Karamin flask na cin abinci, da farantai guda biyu da kuma cokula, fartanya guda daya, adda da tsintsiya guda daidai, bokiti daya da kayan amfani a bandaki, littafin rubutu mai kakkauran bango; shaidar zama dan kasa, takardu na ainihi, da kuma kananan hotuna guda hudu masu farin baya.
NAN