An samu gawarwakin wasu mutane ‘yan gida daya su 4 a wani gonar kiwon kaji da ke Anguwar Street a yankin karamar hukumar Abaji ta Abuja.
CityNews ta baiyana cewa, wani mai gadin gonar kiwon kajin da ake kira da Dominic Peter Adegeze, ‘ya’yansa mata, masu suna Victoria da Judith da kuma dansa dan watanni hudu ne aka ga gawarwakin nasu, sannan kuma matarsa da ake kira da Laruba an garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, ba ta cikin haiyacinta.
Wani ma’aikacin gonar kiwon kajin wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, al’amarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis da ta gabata.
Ya ce wani ma’aikacin gonar da ba shi ba ya je baiwa wasu shanu abinci a cikin gonar, sai ya tarar da gonar a rufe, sai haura inda ya ga mai gadin da iyalansa suna numfashi da kyar kumfa na fita daga bakunansu.
Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda reshen Abuja, Adeh Josephine, ta tabbatar da lamarin, inda ta kara da cewa ‘yansanda na bincike kan lamarin.
(DailyTrust)