Daga: DailyTrust
Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta ce, gazawar gwamnatin tarayya wajen magance fyade da sauran cin zarafin mata da ake shi ke kara ta’azzara matsalar da kuma baiwa masu laifin kariya a kasar.
Wannan na kunshe ne cikin rahoton da aka fitar ranar Laraba, mai taken, “Najeriya: Tafiya mai Wahala; Samun Adalci ga Mata da Yaran da Akaiwa Fyade.”
Amnesty ta ce gazawar gwamnatin na yin abin da ya kamata ya durkusar da wadanda aka ci zarafin.
Rahoton da aka fitar bayan binciken da akai a tsakanin watan Maris na 2020 da Agusta na 2021, ya hada da binciken kararrakin cin zarafin mata da yara, ciki har da ‘yan shekara shida da ‘yan shekara 11 wadanda aka yiwa mummunan cin zarafi.
Osai Ojigho, Daraktar Amnesty International a Najeriya ta ce, “Duk da aiyna dokar ta ta baci kan cin zarafin mata da hukumomi suka yi, fyade ya cigaba da ruruwa, yayin da ake cigaba da kin yin adalci ga wadanda aka ci zarafin, masu cin zarafin kuma an ki hukunta su, sannan daruruwan korafe-korafen fyaden da ba a kaiwa kotuna saboda halin cin hanci da rashawa, da kuma muzgunawa.
“Ba a dauki matakan da suka dace ba wajen magance matsalar fyade a Najeriya, duk da dacewar hakan. Mata da kananan yara na cigaba da samun sarewar guiwa kan tsarin da yake sa su kasa samun adalci, sannan kuma ya ke barin masu aikata laifin suna tsira,”.
Ta kara da cewa, tsoron kar a ki yarda da mutum, ko a kyamaci mutum, na janyo munanan matsalolin yin shirun da yake hana wadanda aka ci zarafin neman adalci.