Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya a Abuja ta sanya ranar 6 ga Disamba, 2021 domin sauraron karar da akai kan cancantar Alhaji Atiku Abubakar ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya.
A ranar Litinin din nan, Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya ta Abuja, ya dage zaman jin shari’ar saboda gazawar masu karar na gyara yanayin shigar da karar da kuma shigar da Babban Lauyan jihar Adamawa cikin karar.
Karar da wata kungiya mai ikirarin tabbatar da demokaradiyya a Afirka mai suna Incorporated Trustees of Egalitarian Mission for Africa (EMA) ta shigar, ta sanya PDP da Atiku da kuma Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami a matsayin wadanda ke ciki.
Kungiyar na tuhumar Atikun da cewa bai cancanci ya tsaya takarar shugaban Najeriya ba, saboda kasancewarsa ba wanda aka haifa a kasar ba kamar yanda yake a sashi na 25(1) da (2) da kuma sashi na 131(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
Sai dai kuma lauyan Atiku, L. D. Nzadon ya musanta batun inda ya ce, Atiku dan Najeriya ne daga jihar Adamawa wanda aka zaba a matsayin gwamna a shekarar 1999, sannan kuma ya zama mataimakin shugaban kasa tsakanin 1999 zuwa 2007.