Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya, TCN, ya fara aikin gyaran ƙarfen tawa ta 16 da ya karye a Ƙauyen Gunduwawa da ke Ƙaramar Hukumar Gezewa a Jihar Kano.
Shugaban Sashin Hulɗa da Jama’a na kamfanin, Ndidi Mbah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da rabawa manema labarai a yau Asabar.
Ya bayyana cewa, ɗankwangilar da ke aikin gyaran ya koma bakin aikinsa a jiya Juma’a tare da bayar da tabbacin cewa, za a kammala gyaran ƙarfen tawar a ranar Alhamis 22 ga watan nan.
Idan za a iya tunawa, wata babbar motar tirela mai ɗauke da dakon kwantena ce ta bi ta kan ƙarfen tawar a ranar Lahadin da ta gabata, inda tai sanadiyar karyewarsa, abin da ya jawo rasa wuta ga al’ummu da dama da ke yankunan Gagarawa, Hadejia da kuma Nguru.