An yanka ta tashi dangane da zaben dan takarar gwamna a jam`iyyar PDP, a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, bayan wata babbar kotun tarayya ta soke zaben fidda gwanin da jam`iyyar PDP ta yi, in da Lawal Dare, ya samu nasarar zama dan takararta na gwamna.
Kotun ta ce ta gamsu cewa ba a bi ka`ida ba wajen gudanar da zaben.
Kotun tarayyar, wadda mai sharia Aminu Bappa, ya jagoranci zamanta a Gusau, babban birnin jihar, ta saurari karar da wasu mutum uku da suka nemi takarar gwamna a tutar jam`yyar PDP a jihar suka kai gaban ta, wanda suka hada da da Ibrahim Shehu Gusau da Malam Wadatau Madawaki da kuma Hafiz Muhammad Nahuce, wadanda suka kalubalanci zaben fidda gwanin na takarar gwamnan suna cewa an tabka kura-kurai tare da taka ka`idojin da kundin tsarin mulkin jam`iyyar ya tanadar, bayan Dr Dauda Lawal Dare ya samu nasara.
Kotun ta ce ta gamsu da hujjojin da lauyan bangaren masu karar, wato Barrsiter Ibrahim Ali ya gabatar, kana ta soke zaben, hukuncin da Lauyan ya ce ya musu dadi.
To sai dai kuma lauyan dan takarar gwamnan da kotu ta soke zaben nasa, Dauda Lawal Dare, wato Barrsiter Masama ya ce akwai bukatar sai bayan sun yi nazarin hukuncin, kana za su san abin yi.
(BBC Hausa)