For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Yanke Wa Dalibai 20 Hukuncin Kisa A Bangladesh

Kasar Bangladesh ta yankewa wasu daliban jami’a su 20 hukuncin kisa a yau Laraba bisa samun su da laifin kisan wani matashi da ya caccaki gwamnati a shafukan sa da zumunta a shekarar 2019.

An gano gawar Abrar Fahad mai shekaru 21 da haihuwa a cikin dakin kwanansa sa’o’i kadan bayan ya rubuta wani sako a Facebook yana caccakar Firaminista Sheikh Hasina kan kulla yarjejeniyar raba ruwa da kasar Indiya.

Wasu ’yan uwansa dalibai 25 da suka kasance mambobin kungiyar dalibai ‘yan jam’iyyar Awami League mai mulki mai suna Bangladesh Chhatra League, sun yi masa dukan tsiya da madokin wasan cricket da sauran abubuwa masu cutarwa na tsawon sa’o’i shida.

Mahaifin Fahad Barkat Ullah ya shaida wa manema labarai a wajen kotun bayan yanke hukuncin, inda ya ce, “Na yi farin ciki da hukuncin,” . “Ina fatan za a aiwatar da hukuncin nan ba da jimawa ba.”

Suma sauran mutane biyar da suka aikata laifin, an yanke musu hukuncin daurin rai da rai.

Babban mai gabatar da kara Mohammad Abu Abdullah Bhuiyuan ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP cewa an shirya kisan ne da gangan.

Duk wadanda aka yanke wa hukuncin kisan ‘yan shekaru tsakanin 20 zuwa 22 ne a lokacin da aka yi kisan, kuma sun halarci babbar jami’ar Koyon Aikin Injiniya da Fasaha ta Bangladesh tare da marigayin, Fahad.

Uku daga cikin wadanda ake tuhuma har yanzu ba a san inda suke ba, yayin da sauran ke cikin kotun a lokacin yanke hukuncin.

Faruque Ahmed, lauyan wadanda ake tuhuma, ya ce za a daukaka kara kan hukuncin.

Ya shaida wa AFP cewa, “Na ji takaicin hukuncin da aka yanke. Bai dace ba,”.

“Su matasa ne kuma wasu daga cikin manyan daliban kasar nan. An yanke musu hukuncin kisa ne duk da cewa babu wata kwakkwarar hujja a kan wasunsu.”

Shi dai marigayi Fahad, ya wallafa wani rubutu a Facebook wanda ya yi ta yaduwa sa’o’i kadan kafin rasuwarsa.

A ciki, ya soki gwamnati da sanya hannu kan yarjejeniyar da ta bai wa Indiya damar daukar ruwa daga kogin da ke kan iyakar kasashen biyu.

An ga Fahad – a cikin faifan bidiyo na CCTV wanda ya yadu a kafafen sada zumunta – yana tafiya cikin dakin kwanan dalibai tare da wasu masu fafutuka na BCL.

Bayan kusan awa shida da faruwar hakan ne, daliban suka dauki gawarsa suka jefar a kasa.

A zanga-zangar da aka yi a kwanaki bayan kisan Fahad an yi kira da a hukunta maharan da kuma haramta kungiyar BCL.

Hasina ta sha alwashin cewa masu kisan za su sami “hukunci mafi girma”.

Kungiyar ta BCL ta yi kaurin suna a cikin ‘yan shekarun nan bayan da aka zargi wasu mambobinta da haddasa kisa, tashin hankali da kuma karbar kudi.

A cikin 2018, an zargi mambobinta da yin amfani da tashin hankali don murkushe wata babbar zanga-zangar adawa da gwamnati.

Comments
Loading...