For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

An Yankewa Malamin Da Ya Yi Wa Dalibansa 13 Fyade Daurin Rai Da Rai

Wata kotu a Indonesia ta yanke wa wani mai makarantar kwana hukuncin daurin rai-da-rai bayan da ta same shi da laifin yi wa ɗaliban makarantar su 13 fyade.

Ta’asar da mai makarantar ya aikata ta bayyana ne bayan da iyalin wata daliba suka kai karar Herry Wirawan a ofishin ƴan sanda bayan da suka gano cewa ta ɗauki ciki.

Bincike ya tabbatar cewa cikin shekaru biyar mutumin ya yi wa daliban fyade – ‘yan matan da shekarunsu na haihuwa ke tsakanin 11 zuwa 16.

Wakilin BBC ya ce ɗalibai takwas sun haifi jarirai 9 a sanadiyyar fyaɗen da mai makarantar yayi musu, saboda ɗaya daga cikin ‘yan matan ta haifi ƴan biyu ne.

Shari’ar ta tayar da hankulan ƴan Indonesia, ƙasar da kimanin yara miliyan biyar ke halartar makarantun kwana na addinin Musulunci.

Sai dai gwamnatin ƙasar ta ba kowace yarinyar da aka yi wa fyade diyyar dalar Amurka kimanin dubu shida.

(BBC Hausa)

Comments
Loading...