An yanke wa tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy hukuncin ɗauri a karo na biyu bayan da aka same shi da laifin kashe kudaden kamfen da suka wuce ƙa’ida a fafutukar sake neman zaɓensa na shekarar 2012.
Sarkozy, dan shekaru 66, wanda har yanzu yana da tasiri a siyasar Faransa, an yanke masa hukuncin daurin shekara 1.
Alkalin da ya yanke hukuncin ya ce, zai iya yin zaman daurin ta hanyar a sanya masa turu na lantarki a kafa, da ake kira da electronic ankle bracelet.
Yanzu Sarkozy yana cikin wani yanayi da ba a taɓa ganin irinsa ba, inda yake da hukunci dauri har guda 2. Haka kuma, a lokaci guda, ya ci gaba da kasancewa mai martaba ga jama’a.
A watan Maris da ya gabata, Sarkozy ya zama shugaban Faransa na farko da aka yanke wa hukuncin zaman dauri na shekaru uku.
Sarkozy ya daukaka kara kan hukuncin kamar yanda ake tunanin zai daukaka kan wannan sabon ma da aka yanke masa a Talatar nan.
Idan har kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin kotunan baya, to akwai yuwuwar za a sanya masa turu na lantarki a kafa yayin zaman hukuncin nasa.