Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, a yau Litinin sun hadu a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Wani shugaba a APC, Dada Olusegun, ya ce Tinubu na kan hanyarsa ne ta zuwa Jos wajen kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na APC.
Wani hoton bidiyo na haduwar ya nuna Tinubu da Atiku a zaune kusa da juna kan wasu jajayen kujeru a yanayi na yin zurfi a hira.
Dukkaninsu su biyun dai na kan gaba-gaba a takarar shugaban kasar da ake yi domin babban zaben watan Fabarairu mai zuwa.